Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba DSP David Misal ya bayyana yadda aka kama wadannan mutanen a wata ganawa da manema labarai.
DSP Misal ya bayyana cewa, “Ahmadu Garba magidanci dan kimanin shekaru 65 da haihuwa, na daga cikin wadanda aka kama bisa zargin lalata da wata karamar yarinyar ‘yar kimanin shekaru 11 da haihuwa. Bayan haka sai Abubakar Bala, dan shekara 37 wanda ke sana’ar wankin mota da kuma Suleiman Ahmadu dan shekara 28 wanda shima aikin gadi ya ke yi, kuma yarinyar ta yi zama da shi tsawon wata 3 yana lalata da ita a cewarsa."
Kakakin rundunar 'yan sandan ya kuma ja hankalin iyaye akan su ci gaba da sa ido da kuma maida hankali kan ‘yayansu saboda yadda zamani ya lalace.
A baya Mallama Binta Khalid Adam, wata uwa kuma yar fafutukar sauya tarbiyar al’umma ta yi karin haske akan dalilan karuwar ayyukan lalata da kuma fyade ga kananan yara da ta kasa su gida uku.
Ta ce kashi na farko sune masu harka da miyagun kwayoyi, na biyu kuma manyan mutane da ke aikata wannan mummunar dabi’a saboda tsubbu. Sai kashi na uku, wanda su kuma hali ne, muddin suka ga wata mace tunaninsu shine su keta haddinta.
Saurari Karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum