Lokacin da baya soja shekaru goma sha biyar ke nan kawo yanzu Hamza Al-Mustapha yace akwai abubuwan takaici da bacin rai da suka faru kamar yadda rahotanni ke bayyanawa. Maganar tsaron cikin gida aikin 'yan sanda ne da 'yansandan ciki da masu fafaren kaya na leken asiri da sauransu, amma ba soja ba. Sai lamari ya fi karfin jami'an tsaron cikin gida za'a sa sojoji.
A wannan zamanin rikicin da ya dabaibaye wasu kasashen Afirka kamar Libiya, makamai sun kwararo zuwa kasashe da dama har da Najeriya. Makamai da kayan soja sun shiga kasuwanni dalili ke nan da yasa mutane na samun kayan yaki su saya a saukake. Rikicin dake faruwa a arewa maso gabashin Najeriya yasa an samu kasuwar makamai.
Yadda wanda ba soja ba ne kuma bashi da horo har ya sa kayan soja ya yi anfani da kayan yaki na soja na ba mutane mamaki. Manjo Hamza yace na farko bai so yayi magana da zurfi akan yadda tsaron Najeriya yake ba. Amma yayi magana akan abu daya tak.
Manjo Hamza yace shekaru da dama wasu yara marayu ne amma an daukesu aikin soja an koya masu sarafa makamai da yin anfani dasu. Amma bisa ga dan laifi kadan da bai taka kara ya karya ba sabili da rashin gatanci sai a koresu daga aiki da wulakanci. An koresu babu aikin da zasu yi kuma babu inda zasu, babu kuma wata hanyar rayuwa sai su nemi hanyar da zasu taimaki kansu. Tunda sun iya sarafa makamai ko su koyawa wasu ko su yi da kansu domin neman abincin da zasu ci. Ba'a la'akari da irin wadannan kuma ba'a bukatar sanin ko su wanene, a ina suke da zama, ko kuma bayan an koresu ba'a damu da yadda za'a taimakesu su samu sana'ar yi. Saboda haka duk wata sana'a da ta zo wurinsu sai su riketa.
Manjo Hamza yace akwai sakaci a kowane bangare. Yakamata a ce ana da bayanai akan kowa musamman irin wadannan mutanen da aka kora. Kowane mutum aka dauka aikin tsaro yakamata a bi digdiginsa. Kuma ko yana cikin aiki ko baya cikin aiki akwai hakkin sanin me yake yi me kuma za'a yi a tallafa masa. Rashin yin hakan hatsari ne. Babu kasar da zata bar hakan ya faru.
Amma Manjo Hamza yayi imanin abubuwa zasu canza.
Akan zargin cewa hukumomin sojan Najeriya basa barin jami'ansu su tunkari wasu matsaloli da kuma zargin cewa wani soja ya ga daya gada cikin kwamandansu yana horas da 'yan Boko Haram, sai Manjo Hamza yace shi ma ya ji maganar.Idan har abun da sojan ya fada gaskiya ne to abun damuwa ne. Idan kuma magana ce kawai ta kawoma wadanda ake yaki dasu rudani to wani makami ne na bangare-bangare.
Akwai manyan sojoji da zasu binciki maganar domin ba'a taru an zama daya ba. Soja kuma kala-kala ne. Akwai na kwarai. Akwai bata gari.
Ga karin bayani.