Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Menene Manjo Hamza Al-Mustapha ya Keyi?


Manjo Hamza al-Mustapha
Manjo Hamza al-Mustapha

Tun da Manjo Hamza Al-Mustapha ya fito daga gidan kaso a ke tayin jita-jita inda ya ke. Wasu su ce koma aikin soja wasu kuma su ce yana aiki da gwamnati. To ko menene ya keyi yanzu?

'Yan Najeriya suna ta kai da kawowa kan ko wane irin aiki Manjo Hamza Al-Mustapha ya keyi tun da ya dawo daga gidan kaso inda ya kwashe kusan shekaru goma sha biyar a tsare.

Wakilin Muryar Amurka Ladan Ibrahim Ayawa ya tambayeshi ya fadawa 'yan Najeriya abun da ya keyi yanzu domin a kawo karshen shatifadi da a keyi. Manjo ya ce tun 1984 ya ke yin abubuwa na taimakawa matasa wajen neman masu makarantau, samar masu da ayyukan yi da neman abun hannu. Kungiyoyinsu ne suke samunsa shi kuma ya ga ya kamata ya taimaka masu. Ya ce yana yawo ne fisabilillahi domin ya taimaka masu.

Manjo Al-Mustapha ya ce arewa na neman taimako. Su 'yan arewa ne kuma ita suke taimakawa. Ita suka sani . Suna kishinta. Kuma suna shirye su taimakawa arewa. Irin taimakon da ya keyi ba wai lallai sai 'yan jiharshi ba ko kuma 'yan cikin gidansu kawai ba. Abun da ya sa gaba shi ne taimakon duk dan arewa dake bukata. Dalili ke nan da ya amince yana zirga-zirga zuwa wurare daban-daban.

Dangane da ko ya koma aikin soja ya ce gwamnatin jihar Legas da ta kaishi kara ta sake daukaka kara. A shirin soji sai duk an gama karar kafin hukumomin soji su yi nasu hukunci. Ganin cewa daukaka karar zata dauki lokaci kana sojoji zasu yi nasu dalili ke nan da ya sa ya ce maimakon ya cigaba da zaman banza yana jira a kammala kara gara ya taimakawa matasa da kuma Najeriya.

Game da cewa wai sako shi nada nasaba da shirin gwamnatin tarayya domin ta yi anfani da shi ta biya muradun wasu manufofin siyasa sai Manjo ya ce ya ji wadannan maganganun. To amma ya ce abubuwan da mutane ke fada basu da hujja. Ya ce kotu ta sakeshi bisa ga cin amana da aka yi masu. Ya ce kotun daukaka kara ta Legas ita ta sakeshi. Ya ce wadanda suka daureshi suka azabtar dashi basu taba tsammanin za'a sakeshi ba.

Manjo ya kalubali tsohon shugaban kasar Najeriya Obasanjo ya fito bainar radio ko teleibijan su yi muhawar kan abubuwan da suka sani na siri game da kasar, to ko har yanzu yana kan bakarsa?. Ya ce yana nan kan bakarsa domin yana da hujjoji da zai tunkari tsohon shugaban da su. Ya ce yin hakan zai wayar da kawunan 'yan Najeriya su san abubuwan da basu sani ba. Muhawararsu zata haskaka abubuwa dake cikin duhu yanzu zata kuma taimaki Najeriya da mutanen dake kasa yanzu.

Ladan Ibrahim Ayawa nada cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:15:00 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG