Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manjo Hamza Al-Mustapha Baya Cikin Kowace Jam'iyya


Manjo Hamza al-Mustapha
Manjo Hamza al-Mustapha

Tun lokacin da Manjo Hamza Al-Mustapha ya fito daga kurkuku mutane ke ta kiransa ya shiga siyasa wasu ma sun ce ya riga ma ya shiga ganin irin tafiye-tayen da ya keyi a kasar Najeriya.

Wakilin Muryar Amurka Ladan Ibrahim Ayawa ya sake zantawa da Manjo Hamza Al-Mustapha kan siyasa da kuma yiwuwar shi Manjo ya shiga siyasa.

Da aka tambayeshi ko ya shiga siyasa sai yace "Ni ba dan siyasa ba ne na fada a da ina fada a yanzu. Ni a yanzu haka bani da katin kowace siyasa a kasan nan. Ni ba dan koina ba ne. Ni dan Najeriya ne. Ni dai a zauna lafiya, a kare hakin bil adama, Najeriyan nan ta samu makoma...Kwadayinmu shi ne arewa ta tashi ta tsaya a kafarta. Shi ne kawai abun da muke yi amma ni ba dan siyasa ba ne. Kuma duk tafiyar da na keyi ban taba furta wani abu na siyasa ba ko na wata jam'iyya ko wani dan takara. Ban taba yi ba".

Dangane da zagayawa da ya keyi cikin kasar an tambayeshi wace nasara zai ce ya samu. Sai Manjo Al-Mustapha yace "Mun samu nasarori masu yawa" Ya ce rahotannin kungiyoyin matasa kan yadda suke hada kawunansu tun daga kananan hukumomi zuwa jihohi da tarayya sun nuna irin nasarar da aka samu. Yace da nasarar ce "zamu yi aiki, kuma kungiyoyi daban daban daga wuraren da bamu je ba suna bullowa daga koina suna kawo kansu a kan a yi aiki dasu"

Burin Manjo Hamza Al-Mustapha shi ne Allah Ya kawo karshen rigingimu da suka taso musamman a arewacin Najeriya "mutane kuma su san cewa suna da 'yancinsu da damansu da zasu yi anfani da shi su samu masalaha yadda zasu taimakawa kansu da kansu"

Game da kalubalantar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yace har yanzu shugaban bai mayarda martani ba kuma yana fatan ya yi hakan. Tambayar da Fani Kayode ya yi ko ina shi Manjo yake lokacin da Obasanjo ya rubuta wasikarsa yace yana Indiya inda ya je neman lafiya. Takardun tafiyarsa suna nan da zasu tabbatar da hakan.

Ga cikakken rahoto.

Manjo Hamza Al-Mustapha Baya Cikin Kowace Jam'iyya - 12:05
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:05 0:00
Shiga Kai Tsaye

Zaben 2023

Karo na biyu kenan a Nijar ake gudanar da bukukuwan Kirsimetin karkashin mulkin soja, inda a bara takunkumin ECOWAS ya dakushe farin cikin
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG