Manjo Hamza Al-Mustapha wanda ke amsa tambayoyin manema labaru jim kadan bayan janye karar da ya kai Sheikh Sanusi Khalil bisa zargin yana horas da wasu domin kwarewa a kisan gilla, yace Obasanjo bai fito kuru-kuru ya ambaci sunanshi a wasikar da ya rubuta ba, amma Sheikh Khalil ya kama suna.
“Shi Obasanjo yayi nasa a watan Decemba, shi Sanusi Khalil ya fara yi a kaina a watan Satumba, shi kuma Obasanjo da yayi, sai ya rubuta amma babu sunana a ciki, kwatancen da yayi a wasikar, da ni yake, amma wadansu sharudda na tsoron shari’a, na tsoron mene ne kazafi, da kuma sanin nauyinsa, shiyasa yaki fadan sunana. Amma duk da haka, idan akwai wani Ofis, mai kula da ‘yancin dan Adam dake bincike akan wannan wasikar, idan sun gama zaku ga me zanyi. Shi kuma Sanusi Khalil sunana yake kira, da abubuwa na kazafi,” a cewar Manjo Hamza Al-Mustapha.
To ko menene yasa Hamza Al-Mustapha ya janye wannan kara?
“An janye kara saboda ta inda ya hau, yayi maganar da yayi na kazafi, ya hau wannan mumbarin ya kuma janye, da kuma dalilai, kuma a yau wannan kaset din suna nan, kowa yana ji yana gani, wadannan dalilan muka bi, aka zo aka janye wannan maganar.
Lauya Muhammed Sani Katu, shine mai kare wanda aka kai kara.
“A kullum, muna gina tarbiyyarmu ne akan koyarwar da malaman mu suka gina mu akai, kuma zamu mayarda shi akan abubuwa guda biyu. Da jarrabawa da ibada. Abunda ya faru tsakanin bayin Allah dinnan, ‘yan uwa ne, mu dauke shi a matsayin jarrabawa. Yanzu mun samu anyi sulhu tsakaninsu, ashe kuwa ya zama wajibi mu godewa Allah.
Shima Sheikh Sanusi Khalil yayi godiya gameda janye wannan kara.
“To AlhamdulilLahi godiya ta tabbata ga Allah. Dama al-amura biyu ne, kaddara mai kyau da mara kyau duk daga Allah suke. Ya faru kuma Allah Ya kawo karshen al-amari.”