Shugaba Jonathan yace shi bashi da wani ra'yi na kashin kansa gameda sakamakon taron. Yace kuma ya nace a yi taron ne bayan samun amincewar 'yan Najeriya da suka ce a gaggauta taron. Lokacin bude taron Shugaba Jonathan ya yi alhini ga mutuwar wasu yayin da suke daukar jarabawar neman aiki da hukumar shige da fici ta Najeriya ranar Asabar da ta gabata. Ya bukaci a yi shiru na minti daya saboda karrama wadanda suka mutu a turmutsitsin da ya faru.
Shugaba Jonathan ya fadi mahimman abubuwa guda uku da suka sa yai yi tsayin daka kan tabbatar da an shirya taron. Na daya ba za'a ki yin taron ba domin akwai zababbun 'yan majalisa. Na biyu domin an yi tarurruka can baya ba zai hana taron ba domin matsaloli da aka samu a 1960 ba irin na yanzu ba ne a shekarar 2014. Abu na uku yace baya jin taron zai kawo fadada kabilanci ko bangaranci. Shugaban ya bukaci 'yan majalisa su duba batun jefa kuri'a biyu bisa uku wato "referendum" a turance. Ba mamaki za'a bukaci yin hakan bayan kammala taron.
Jonathan yace taron ka iya tabo batun mallakar arzikin yanki, karin jihohi, da kananan hukumomi da dai wasu batutuwa makamanninsu. Yayi fatan taron zai hada kasar ba rabuwar kawuna ba.
Shugaban taron Justice Idris Kutigi ya godewa Jonathan domin bude taron da kansa, amma bai tabo wani alkawari na yadda taron zai gudana ko kaucewa abubuwan da ake fargaba ba.
Isa Tafida Mafindi daya daga cikin masu halartar taron yace duk abun da a keyi akwai ka'ida. Yace kafin a tsayar da wata magana sai ta samu kuri'u biyu cikin uku na duk wakilan. Domin haka babu wani abun da zai tsaya idan bai samu karbuwa a wani gefen ba. Misali idan wakilan kudu maso kudu suka ce suna son duk arzikin man fetur ya tafi wurinsu yaya za'a yi dasu a arewa? Mafindi yace idan zasu samu kuri'u biyu bisa uku da duk kasar sai a basu.
Wasu 'yan Najeriya sun ce a yi takatsantsan domin kada taron ya kawo bangaranci ko raba kawunan mutanen kasa. Manjo Hamza Al-Mustapha yace a yi hankali domin abu kankani ka iya sa ashana ta kama domin akwai munafukai da dama da suke son a raba kasar ko kuma a ci mutuncin wani bangare. Yace idan akwai gaskiya to a yita komi dacinta idan zata kawo gyara da tabbatar da zaman lafiya.
Ga karin bayani.