Wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya ya zanta da Sheikh Sanusi Khalil akan taron sulhun da kuma sakamakonsa. Yace ranar Alhamis da ta gabata aka yi taron kuma ya bada goyon baya ga duk abun da aka cimma a taron.
An zauna a karkashin jagorancin Dr Ahmed Mahmud Gumi. Bisa ga bayanan da Manjo Hamza Al-Mustapha yayi ya bayyana cewa baya horas da kowa tarbiyar kashe wadanda gwamnatin tarayya take ganin suna yi mata barazana. Manjo Hamza bashi da hannu wajen horas da matasa domin su kashe mutane. Bisa ga bayanan, Sheikh Khalil yace waccan magana da yayi akan Manjo Hamza Al-Mustapha ya janyeta. Gaskiyar magana yanzu ita ce Manjo Hamza yana tare da al'umma yana yaki da cin zalunci a kasar kuma yana bada irin nashi gudunmawa.
Wakilinmu ya tambayi Sheikh Khalil shin baya jin janye maganar zata sa masu binsa su soma dari-dari da shi. Sai ya kada baki yace "shi yana kara godiya ga Allah da ya kaddara wannan abu" Yace karar da Manjo Al-Mustapha ya kai ta zama rahama gareshi. Yace kafin zaben 2011 Allah ya sa yayi bayanan wasu abubuwa kuma babu wanda bai bayyana ba. Yace idan an gabatar da abubuwa ashirin ya zama daya ne kawai ya zama kuskure kamata yayi shi ya ji tsoron Allah ya fito ya janye maganar.
Dangane da ko sabili da tsoron kada kotu ta daureshi ne yasa ya janye maganar Sheikh Khalil yace kowa nada daman ya fadi ra'ayinsa akan maganar. Addu'ar da zai yi shi ne Allah ya haskaka zukatan irin wadannan mutanen. Kuma tun da shi Manjo Al-Mustapha yayi bayani kuma ya yadda da sulhun da aka yi to ai magana ta kare.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.