Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa ta bi Sawun Majalisar Wakilai


Ginin majalisun tarayyar Najeriya.
Ginin majalisun tarayyar Najeriya.

Majalisar Dattawa ta bi sawun majalisar wakilai wadda tuni ta amince da karin wa'adin dokar ta baci a jihohin Adamawa, Borno da Yobe

Bayan cecekucen da aka yi makonni ana yi yanzu dai majalisar dattawan Najeriya ta amince da karin wa'adin dokar ta baci a jihohin Adamawa, Borno da Yobe amma da wasu sharudda.

Bayan sun kwashi sa'o'i biyar suna tuntubar juna a asirce 'yan majalisar dattawa sun bi sawun 'yanuwansu na majalisar wakilai inda suka amince da karin wa'adin dokar ta baci a jihohin nan uku dake cikin dokar.

Daya daga cikin sanatocin da abun ya fi shafa Ali Ndume yace sun bada sharudda guda takwas masu karfi. Daya daga ciki sharuddan shi ne kowane wata sai sun baiwa majalisar rahoton cigaba ko matsalolin da aka samu. Idan majalisar bata gamsu ba to tana iya soke dokar. Na biyu sai an kara sojoji tare da duba wadanda suka cancanta a cikin kungiyar JTF ta fararen hula domin a daukesu aikin soja. Kana a kara wa sojojin kayan aiki. Idan kuma ta kama shugaban kasa ya gabatar da sabon kasafin kudi domin aikin yakin to yayi hakan.

Yanzu wajibi ne shugaban kasa ya fito da tsarin farfado da tattalin arzikin yankin na arewa maso gabas. Yayi tsarin da za'a yi yanzu cikin gaggawa da kuma tsarin da za'a yi na dindindin.

Sanata Alkali Jajere daga jihar Yobe yace siyasa da hakkin wadanda suke wakilta suka sasu daukan matakin da suka dauka duk da cewa a zukatansu basu amince ba. Yace ba zai iya tuna ranar da ransa ya baci yana takaici ba irin wannan ranar. Sanata Jajere yayi takaici har kuka yayi. Yace kukan dole ne domin bakin cikin yadda ake kashe al'ummar da shi yake wakilta da yadda aka hanasu walwala. Yace ya tambayi kansa shin shi ya zama wakili nagari. To amma kodayake ya nuna bakin cikinsa da damuwarsa shi kadai cikin dattawa 109 a shirin dimokradiya dole masu rinjaye su samu hanyar da zasu bi su kuma marasa rinjaye su hakurada yin korafi.

Batun ko an murdewa sanatocin arewa hannu ne yayin da suka sha alwashin ba zasu amince da karin ba, sanata Jajere yace ba murde hannu ba ne. Yace wasu dalilai ne da aka kawo wadanda basa son a yi anfani dasu a cutar da mutanensu fiye da yadda suke cutuwa yanzu. Dalilan sun hada da cewa idan ba'a kara wa'adin ba sojojin dake can kan daga ba zasu iya aiki ba, kamar an karya masu gwiwa ke nan. Haka kuma kasashen da zasu shigo su yi aiki ba zasu iya ba idan babu dokar domin Najeriya kasa ce mai 'yanci.

Tun da aka fara dokar ta baci an kashe kudade sama da nera tiriliyon biyu. Sanata Umaru Dahiru shugaban sanatocin arewa yace basu gamsu da yadda aka kashe kudaden ba kuma sun gayawa sashen zartaswa su binciki yadda aka kashe kudin. Yace yanzu idan za'a yi aiki a yi idan kuma ba za'a yi ba a bari.

Ga rahoton Medina Dauda.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG