Yana mai cewa “sansanin da aka ce za’a kafa a Chadi, ai musan kasar Chadi ba kasar damokradiya bane,yaushe ne suka taba yin zabe na damokradiya na karshe zuwa yau, kama karya akeyi a wannan kasar, ita ma kasar Kamaru ba kasar damakradiya bane tunda, tun bayan Ahmadu Ahijo, wannan shugaban da yake kan mulki shakarun sa yafi sabain har yanzu yana kan mulki.”
Ya kara da cewa “da kasar Chadi da Kamaru,karnukan farautane na kasar Faransa don haka dole ne kasar Faransa duk abunda zata yi sai ta saka su a ciki,koda yake suma ba wani dadi suke ji kare taba,amma a hakan nan dama suna tare da ita badan ta ji dadi bane don su saci dukiyarta ne kuma suyi amfani da harabanta ne.
Shi kuwa Manjo Yahaya Shinku mai ritaya yace ”kwalliya zata iya biyan kudin sabulu don saboda barazanar da kungiyar boko haram takeyi na hare-hare daga wannan bangare inda ka kula duk kasashen dake sagaye damu kasashe ne masu Magana da harshen Faransanci ne, renon Faransa, saboda haka suna jin magananta ta kuma taimakamasu dai-dai yanda yakamata, to saboda kada alamarin boko haram din ya kazanta ya fadamasu yanda suma ba zasu iya samun kwanciyar hankali ba, saboda haka abun zai yi tasiri zasu dauki abun da gaske, kuma masamman zai kasance baida nisa daga wannan zango na ‘yan boko haram wanda yake yankin arewa maso gabashin Najeriya.”
Shi kuma Mr. Gem Pam na kungiyar hada kan al-umma na Unity Forum na goyon bayan wannan yunkuri kamar yanda ya kara da cewa “Chadi tazama kamar tushen ‘yan tawaye ne domin idan ka duba shekaru baya duk kokarin da akayi na son cire shugabansu, da Najeriya ta taimakawa Chadi, zai ‘yan tawayen suka fara taimakawa ‘yan tawaye daga namu bangaren,kuma Libiya nada Matsala ana kawo makamai daga Libya a biyo dashi ta Chadi.”