Ranar Lahadin da ta gabata daya daga cikin iyayen yaran ya rasu sakamakon bugun zuciya da ya kamu da shi.Tun lokacin da aka sace 'yan matan wasu alamura da dama suka faru wadanda suka hada da mutuwar wannan mahaifin.
Kungiyoyi masu karfi da masu zaman kansu a ciki da wajen Najeriya sun yi zanga zanga akan sace yaran. Haka ma gwamnatocin duniya gaba daya suka yi tur da lamarin yayin da wasu kasashe suka kawowa kasar Najeriya doki domin a gama da kungiyar Boko Haram.
Mr. James Yemen mazaunin karamar hukumar Chibok shi ne danuwan mutumin da ya rasu yace rashin ganin 'ya'yansa mata guda biyu ya tayar masa da hankali matuka. Lamarin da ya kara tada masa da hankali shi ne rashin ganin 'ya'yansa a cikin bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar kwanaki. Marigayin yana da 'ya'ya takwas da suka hada da 'yan matan biyu da aka sace.
Mr James Yemen yace rashin labarin yaran ya sasu cikin tunane kullum. Sun rasa abun da zasu yi. Yace danuwan nasa yana cikin tunane koyaushe hatta abinci ma baya ci. Wasu da yawa idan an basu abinci ma ba zasu ci ba sabili da zurfin tunane.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.