Tsarin mulkin ya kuduri a samu kuri'u kashi biyu cikin kashi uku kafin a tsayar da kowane kuduri. Shugaban sanatocin arewa Sanata Umaru Dahiru yace zasu yi iyakacin kokarinsu domin su yi watsi da karin wa'adin dokar. Idan kuma sun fadi to shi ke nan. Majalisar zata yi zamanta wannan makon domin ta jefa kuri'a akan dokar ta bacin.
Kudurin kara dokar ta baci a jihohi uku na arewa maso gabas tuni ya samu goyon bayan 'yan majalisar wakilai su dari uku da sittin. To amma kudurin na samun suka daga sanatocin da suka fito daga jihohin da dokar ta shafa da ma wasu makwaftansu.Dattijon NEPU Huseini Gariko ya caccaki 'yan majalisar wakilan da suka amince da karin wa'adin dokar. Yace duk kashe-kashen da ake yi sai da aka kafa dokar ta baci suka karu. Yace idan 'yan majalisa na kaunan mutane me ya hana su gayawa kowane gwamna ya kafa dan kato da gora. Yace 'yan majalisa ba aikin mutane su keyi ba. Kudi suke karba kana su kafa dokar da zata cuci mutane.
Sabo Imam Gashuwa daga jihar Yobe bai ga fa'idar dokar ba.Yace tun da jami'an tsaro na yin babakere dole ne su baiwa 'yan majalisa bayanan da zasu sa a kara wa'adin dokar. Dokar ta kara sa al'ummar yankin cikin mawuyacin hali kana ayyukan ta'adanci karuwa suka yi a karkashin dokar. Yace bayan kafa dokar sau biyu an kashe dalibai a jihar Yobe. A jihar Borno an sace yaran kamaranta kuma sau da dama an kashe mutane fiye da dari biyu biyu kowane lokaci.
To saidai daya daga cikin 'yan taron kasa mai wakiltar yankin Yarima Muri Isa Tafida na ganin alherin tsawaita wa'adin. Dokar ta baci ita ta taimaka har wasu kasashen waje sun shigo su taimaka. Nan da wata biyu zasu kammala aikinsu. Idan an kara wa'adin dokar da wata shida kasashen waje zasu yi aikin wata biyu sauran watanni hudun dole kasashen su kawo taimako su ingiza gwamnatin tarayya. Idan an bar jihohin babu dokar ta baci nan da shekara talatin ba zasu shawo kan ta'adanci ba.
Yayin da ake ci gaba da muhawara sai kuma aka rubuta wata wasika zuwa jihar Binuwai wai 'yan Boko Haram zasu kai hari akan makarantu biyu. Kawo yanzu dai an dauki tsauraran matakan tsaro.
Ga karin bayani.