Wani mazaunin birnin Jos wanda ya wuce ta kusa da babban Asibitin Jan Kwano yace yaga ana ta wucewa da mutanen da suka jikkata daga harin, amma jami’an tsaron Najeriya sunki bari jama’a su shiga cikin asibitin.
Dauda Yusuf wani dan jarida ne a birnin Jos. “Jama’ar dake kusa da inda abun ya faru sunce sunji ginunuwan da suke ciki sun girgiza.”
Faruwar wannan lamari ke da wuya, ma’aikata suka fara tattara kayansu suna guduwa gida.
Mr. Yusuf yayi karin bayani akan tsaurara matakan tsaro a birnin na Jos.
“A kwana-kwannan saboda irin abubuwan da suka faru a Abuja, gwamnati ta dage akan harkokin tsaro, an saka jami’an tsaro a ko ina.”
Kasuwar Taminos dai itace babbar kasuwa a birnin Jos, inda jama'a da dama daga ciki da wajen birin ke zuwa domin saye da sayarwa.
Wata mata da muka saye sunnanta, kuma take wajen a lokacin da Bom din ya tashi, tayi karin bayani "ana zuba gawarwakin mutane a wilbaro, akwai mutane da yawa wadanda sun ji raunuka, wadansu a keke aka zuba su".
Ya zuwa yanzu babu wanda ya fito ya dauki alhakin wannan hari.