Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari Jos


Mutane na kallon wajenda Bom ya fashe a birnin Jos, dake Jihar Filato.
Mutane na kallon wajenda Bom ya fashe a birnin Jos, dake Jihar Filato.

​Misalin karfe uku na rana agogon Najeriya, wasu tagwayen boma-bomai sun fashe a kusa da kasuwar Taminos dake birnin Jos a Jihar Filato, wanda ya jawo asarar rayuka da jikkata wasu.

Ya zuwa yanzu babu bayani akan irin barnar da wannan Bom yayi, amma wani mazaunin birnin Jos wanda ya wuce ta kusa da babban Asibitin Jan Kwano yace yaga ana ta wucewa da mutanen da suka jikkata daga harin, amma jami’an tsaron Najeriya sunki bari jama’a su shiga cikin asibitin.

Dauda Yusuf wani dan jarida ne a birnin Jos. “Jama’ar dake kusa da inda abun ya faru sunce sunji ginunuwan da suke ciki sun girgiza.”

Faruwar wannan lamari ke da wuya, ma’aikata suka fara tattara kayansu suna guduwa gida.

Mr. Yusuf yayi karin bayani akan tsaurara matakan tsaro a birnin na Jos.
“A kwana-kwannan saboda irin abubuwan da suka faru a Abuja, gwamnati ta dage akan harkokin tsaro, an saka jami’an tsaro a ko ina.”

Kasuwar Taminos dai itace babbar kasuwa a birnin Jos, inda jama'a da dama daga ciki da wajen birin ke zuwa domin saye da sayarwa.

Wata mata da muka saye sunnanta, kuma take wajen a lokacin da Bom din ya tashi, tayi karin bayani "ana zuba gawarwakin mutane a wilbaro, akwai mutane da yawa wadanda sun ji raunuka, wadansu a keke aka zuba su".

Ya zuwa yanzu babu wanda ya fito ya dauki alhakin wannan hari.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG