Kodayake majalisar bata bayyanawa manem labarai ba abubuwan da suka tattauna, masu kula da alamuran harkokin tsaro suna ganin sha'anin tsaro na kan gaba da kuma shirin mika mulki ga sabuwar gwamnati.
Muryar Amurka ta tuntubi Janar Abdulrazak Umar tsohon soja kuma mai sharhi akan lamuran tsaro ya bada haske akan lamarin, musamman yayi bayani akan irin abubuwan da ake tattaunawa inda aka samu irin yanayi na yanzu.
Janar Umar yace na farko abun da ake yi shi ne yaya za'a shirya mika sandar mulki daga wannan bangaren zuwa wancan ba tare da tashin hankali ko yamutsi ba.Abub na biyu shi ne a yi tunanen abun da ka iya biyo bayan mika sandar mulkin.
Dangane da yin la'akari da halin da kasar ke ciki saboda aika-aikar 'yan Boko Haram Janar Umar yace a lura da abun da shi sabon shugaba mai jiran gado ya fada akan 'yan matan Chibok da har yanzu suna hannun 'yan Boko Haram. Sabon shugaban yace basu san inda suke ba. Basu da labarin ko suna da rai da kuma irin halin da suke ciki. Kana Janar Buhari yace basu san irin karfin da 'yan Boko Haram suke dashi ba ko lagonsu. Ya nuna ba zai iya yin wani abu ba sai linzamin shugabanci ya shiga hannunsa. Su wadanda zasu karbi mulki dole su yi tunane akan wadannan abubuwan.
Su ma da zasu mika ragamar mulki abun da zai damesu shi ne idan wadannan mutanen APC suka shigo gwamnati yaya zasu jimasu. Zasu ji tsoron yiwuwar muzguna masu.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.