Rahotanni daga Najeriya na cewa za a sauya manyan jami’an kamfanin matatar man Najeriya ta NNPC, sannan za a bincike hadahadar man da kamfanin ya gudanar.
Kamfanin dillancin labaran Reuters wanda ya tattauna da wani kusa a jam’iyyar APC, ya ruwaito cewa za kuma a binciki asusun kamfanin domin a maido kimarsa.
Har rahotanni na cewa za a tsaga kamfanin zuwa gida hudu kamar yadda aka tsara sabon kudirin yin garambawul ga kamfanin.
Kamfanin dillancin labaran na Reuters ya ruwaito cewa ‘yan jam’iyyar ta APC za su cire ministan man fetur daga manyan jami’an gudanarwar kamafnin domin a kawar da yuwuwar samun yin katsalandan a siyasance.
A cewar rahotanni fannin man fetur zai samu bangarenshi yayin da fannin iskar gas zai samu nashi bangaren kana bangaren da ya shafi kula da bututun mai zai samu nashi kulawa ta musamman, sannan za a samar da wani bangaren na hudu da zai dinga kula da duk bangarorin.
Ana kuma sa ran za a gabatar da wannan bukatar a gaban ‘yan majalisun kasar a farkon shekara mai zuwaa a cewar majiyar da ta gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.