Tare da yin la’akkari da yadda rikicin Boko Haram ya kassara tattalin arzikin yankin arewa maso gabashin Najeriya, wasu kungiyoyo masu zaman kansu, sun yi kira ga zabbabiyar gwamnatin APC da ta kafa wata hukuma da za ta taimaka wajen farfado da tattalin arzkin yankin.
Kungiyoyin sun nuna bukatar haka ne ganin yadda aka yiwa wasu sassan Najeriya da suka yi fama da matsaloli a baya.
“Za mu tura kudirin doka zuwa majalisar dokokin Najeriya domin a kafa wata hukuma da za ta lura da bunkasa yankin arewa maso gabashin kasar nan.” In ji Hamisu Idris Maidugu na daya daga cikin kungiyoyin.
Ya kara da cewa idan aka duba a baya, an kafa hukumar da ke bunkasa yankin Niger Delta a lokacin da aka samu wasu mataloli a yankin.
“Saboda haka idan ka duba mu mun fi su ma shiga matsalar rikici domin gwamnatin jiha ba za ta iya tunkarar wannan matsalar ba, dole ne abin ya biyo ta hanyar gwamnatin tarayya inda za a saka ministan da zai lura da yankin.” Maidugu ya kara da cewa.
A cewar sa tuni sun fara neman ‘yan majalisun da ke wakiltarsu game da wannan bukata tasu sannan ya ce za su rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa da kuma shugaban majalisar dattawan kasar kan wannan bukata.
Ga karin bayani a wannan rahoto: