Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja ya karyata labarin da ake bazawa cewa yana son ya raba wasu masarautun jihar.
Ana rade-radin cewa gwamnan zai kara wasu masarautu a jihar kafin ya mika mulki ga sabuwar gwamnati.
Yanzu haka dai labarin ya mamaye jihar inda ake cewa tuni ma gwamnan ya tura bukatarsa na raba masarautar Minna gida uku ga majalisar dokokin jihar.
Rahotannin dai na cewa zai raba kontagora gida uku kana ta Bida za'a tsagata gida biyu.
Hakazalika, akwai bayanai da ke cewa shi kansa gwamna Aliyu yana neman zama magajin garin Minna.
To amma a taron manema labarai jami'in yada labarai na gwamnan Mr. Israel Ebije ya ce babu kanshin gaskiya a labarin.
Ya ce a saninsa cikin shekaru takwas da suka yi a mulki irin wannan batun bai taba tasowa ba.
Kuma idan ma za'a yi hakan akwai hanyoyi da dama da dole sai an bi yana mai cewa menene ya sa sai yanzu maganar za ta taso domin abu ne dake bukatar tuntubar masu ruwa da tsaki.
Ebije ya kuma yi kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu.
Amma duk da bayanin na jami'in labaran gwamnan, masu alaka da sarauta hankalinsu bai kwanta ba.
Tsohon shugaban karamar hukumar Chanchaga Alhaji Ahmed Dogara dake da alaka da masarautar Minna ya ce idan an ji jita-jita akwai gaskiya cikin maganar.
Ya ce mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar ne ya gabatar da kudurin raba masarautun.
To sai dai majalisar dokokin jihar ta ce kawo yanzu babu maganar a gabanta amma basu san abun da zai faru kafin karshen wa'adinsu ba.
Ga karin bayani daga Mustapha Nasiru Batsari.