Lamido Umar Zakari Ajiyan Gombe ya fara da cewa shi dan PDP ne sak kafin ya taya Janar Buhari murnar cin zabe da kuma yi masa fatan alheri.
Lamido ya yi alkawarin cewa za su bar PDP su koma APC ba ko domin kwadayi ko wauta.
Amma ya ce za su yi masa adawa sak, idan ya yi daidai za su yaba masa. Idan kuma bai yi ba za su fada.
Ya ce kowane wata shida za su tambay eshi shin ko lantarki ya samu kuma matasa sun samu aikin yi ko shin an samu tsaro.
Ya ce aikin dan adawa ne ya dinga tunawa shugaba alkawuran da ya yiwa mutane.
Dangane da dalilan da suka sa Janar Buhari ya yi nasara akan PDP, Ajiyan Gombe ya ce dadewa da jam'iyyar ta yi akan mulki na shekara 16 ya sa mutane suka gaji da su.
Na biyu ya ce ba'a yi sa'a ba domin wadanda suka rike jam'iyyar da gwamnati ba 'yan siyasa ba ne. 'Yan tsintuwa ne kuma 'yan shagwaba ne. Yace duk rikon mulkin da aka yi an yi rikon ne irin na rashin iyawa. Yace kowane irin aiki aka yi akwai siyasa na yadda za'a tafi da jama'a. Saboda haka duk abun da aka fadawa 'yan Najeriya wanda ya san siyasa ba zai gamsu ba.
Akan wadanda suka canza zuwa APC ko kuma wadanda suke nufin hadewa da Janar Buhari daga PDP, Ajiyan Gombe ya ce hadewarsu da Buhari annoba ce ga APC da shi Buharin.
Ya ce sun tabbatar akwai lokacin da za su kai ruwa rana domin irinsu ne suka cika jam'iyyar 'yan kaddarar, yahna mai cewa irinsu ne irinsu ne 'yan shagwaba, ba 'yan siyasa ba ne.
"Yyaya za'a ce domin jam'iyyarka ta fadi ka ce ba zaka yi adawa ba kana son ka sha dadi." In ji Ajiyan Gombe.
Ajiyan Gomben ya kuma kara da cewa, watakila abin da ya faru zai gyara "'yan shagwaba" da basu yi mulki da kyau ba yana mai cewa yana fata za su koyi kyakyawan darasi.
Akan cewa wai su a Gombe za su koma APC, ya ce menene dalilin komawa?
"Wadanda suke son komawa ga fili ga doki amma su, suna nan daram cikin PDP."
Ya kara da cewa suna jira za su yi adawa, Idan wahala ce su sha kamar yadda 'yan APC suka sha.
Shawararsa ga gwamnan Gombe ita ce ya cigaba da aikin da yake yi ya kuma tsaya cikin PDP idan yana son ya kare mutuncinsa ya kuma zama mutum.
Ga kari rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya.