A zantawa da ya yi da manema labarai a karon farko bayan an zabe shi gwamna Simon Lalong ya yaba da yadda jama'ar Filato suka bashi goyon baya.
Ya ce ya yi farin ciki domin nasararsa ta nuna masa cewa addu'ar mutanen Filato ya kawo canjin da aka samu.
Abubuwa biyu mafi mahimmanci da ya sa a gaba yanzu a cewarsa su ne biyan albashin ma'aikata da kuma hada kawunan jama'a yana mai cewa wasu ma'aikatan sun yi watanni goma ba'a biyasu ba.
Filato na neman zaman lafiya idan ba'a biya mutane hakkinsu ba da wuya a kama hanyar zaman lafiya.
Da zara ya shiga ofis zai nemi yadda zai biya ma'aikata. Idan za'a ma ba gwamnatin bashi zai fara biyan mutanen.
Akan hada kawunan mutane ya ce sun fara kemfen da kabilu 52 sun kuma nemi hanyoyin da za'a zauna lafiya.
Da zaran ya kama aiki sabon gwamnan ya ce zai zai kafa kwamitin kabilu 52 wadanda za su zauna su shirya hanyoyin da za su samar da zaman lafiya.
Shi ma abokin takararsa na PDP da ya fadi zaben Sanata Gyang Pwajok cewa ya yi hadin kan daukacin mutanen jihar ne zai kawo masu cigaba.
Ya ce ya yadda Allah ne ke bada mulki ga wanda ya so a kuma lokacin da ya zaba.
Pwajok ya ce za su mika hannun zumunci ga dan'uwansu sabon gwamnan ganin cewa shugabanci na bukatar gudummawar mata da maza saboda daidaita harkokin mulki da cigaban al'umma.
Ya ce mun hakikance cewa da hadin kanmu za mu iya gina jihar Filato.
Ga rahoton Zainab Babaji.