Yanzu haka ,an fara sauraron karar da gwamnan jihar Taraba dake jinya Danbaba Suntai ya shigar na kalubalantar matakin da yan majalisar dokokin jihar suka dauka na cewa gwamnan ya koma ya cigaba da jinya,shi kuwa mataimakinsa Garba Umar ya cigaba da riko a matsayin mukaddashin gwamnan,matakin day an gaba-gaban komo da gwamnan ke nuna rashin amincewa.
WASHINGTON, DC —
A zaman kotun da akayi a cikin tsauraran tsaro, lauyoyin Gwamnan da kuma na bangaren ‘yan majalisar sun tafka doguwar muhawara da kuma bukatar dage sauraron karar domin basu damar kimsawa. Alkalin kotun Justice Andrew ya amince da wannan bukata, kuma ya dage shari’ar zuwa ran Talata mai zuwa.
Wannan na zuwa ne,yayin da wani sabon rikici ya kunno kai a kungiyar lauyoyin jihar, inda wasu lauyoyi suka fara maida martini game da kalaman da shugaban kungiyar lauyoyin jihar yayi na cewa gwamnan ya warke,batun dam asana harkar shari’a ke cewa bai dace ba.
Shugaban kungiyar Lauyoyin Najeriya na reshen jihar, daya daga cikin lauyoyin Danbaba Suntai din, Barrister Ibrahim ya jagoranci wasu lauyoyi zuwa wajen gwamnan, sannan ya fito zuwa wajen manema labarai yana mai cewa Gwamna Danbaba ya warke. Wannan kalami dai ya jawo martani daga lauyoyin daya bangaren.