Bayan wannan doguwar Muhawara, alkalin kotun Justice Ali Ibrahim Andaya Tsoho ya dage sauraron shari’ar, har zuwa ranar 30 ga wannan wata na Satumba domin cigaba da sauraron shari’ar.
SAN Yusuf Ali wanda yana daga cikin lauyoyin dake kara ‘yan majalisar, yayi bayanin ko meyasa lauyoyin suke bukatar zuwa kotun daukaka karar.
“Mu matsayin mu shine, batun da ake magana akai, sabon abu ne a dokokin kasar nan, don haka ne yakamata a mika batun ga kotun daukaka kara, wato Court of Appeal, domin jin nata ba’ahasin, “ a cewar SAN Yusuf Ali. “Kuma muna kyautata zaton samun nasara a wannan shari’a.”
Yanzu dai hankulan manazarta harkar shari’a ya koma ga dambarwar siyasar jihar Taraba, kuma lokaci ne ke tabbatar da abunda ka iya faruwa a lokacin da Alhaji Garba ke cigaba da jan ragamar jihar tare da kwamishinonin da suka ki ballewa.