Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Amurka Ta Amince Da Sama Da Dala Triliyan 1 Kasafin Kudin 2014


Capitol Hill
Capitol Hill

A jiya Lahadi manyan shugabannin Majalisar Dokokin Amurka suka amince da kasafin kudin da gwamnatin tarayya zata kashe a shekarar 2024 na dala triliyan 1 da digo 6.

WASHINGTON, D. C. - A wata yarjejeniyar da ta tserar da tsayawar ayyukan gwamnati na dan wani lokaci a cikin watan nan da ake ciki, a cewar kakakin Majalisar wakilan Amurkan Mike Johnson.

Mike Johnson (R-LA)
Mike Johnson (R-LA)

Johnson wanda dan jam’iyar Republican ne, ya bayyana cikin wata wasika da ya aikewa ‘yan Majalisar Dokokin, cewa, gagarumin adadin ya hada da dala biliyan 886 da zai je ga bangaren tsaro, sai dala biliyan 704 na ayyukan da basu shafi tsaro ba.

Tun a watan jiya ne dai kudurin kasafin kudin na tsaro ya sami rattaba hannun Shugaba Joe Biden inda kudurin ya zama doka, bayan kare yadda za’a kashe kudaden tsaron.

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden

Wata sanarwar hadin guiwa da shugaban masu rinjiya a Majalisar Dokoki, dan jama’iyar Democrat Chuck Schumer da Shugaban ‘yan jama’iyar Democrat a Majalisar wakilai Hakeem Jeffries suka fitar, tace, kudaden da za’a kashe a bangarorin da basu shafi tsaron ba, zasu kula ne da muhimman bangarori kamar na hakkokin tsofaffin ma’aikatan da suka manyanta, sha’anin kiwon lafiya, da tallafin abinci mai gina jiki, daga kudaden da ‘yan jama’iyar Republican suka nemi a daddatse.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG