Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Tayi Tayin Tallafawa Gabon Komawa Mulkin Demokradiyya


Shugaban Rukon Kwarya, Janar Brice, Ranar Da Aka Rantsar Da Shi Libreville, Gabon, September 4, 2023.
Shugaban Rukon Kwarya, Janar Brice, Ranar Da Aka Rantsar Da Shi Libreville, Gabon, September 4, 2023.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya ya shaidawa shugaban sojojin Gabon cewa hukumomin Majalisar Dinkin Duniya a shirye suke su tallafawa kasar yayin da take kokarin komawa kan tsarin mulki bayan juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin iyalan Bongo na tsawon shekaru 56.

WASHINTON, D. C - Jami’an soji sun kwace mulki a ranar 30 ga watan Agusta, inda suka soke zaben da aka kammala ‘yan mintoci bayan sanarwar cewa Shugaba Ali Bongo ne ya sake lashe zaben, zaben da suka ce bai inganta ba. Bongo wanda ke kan karagar mulki tun shekara ta 2009 ya gaji mahaifinsa Omar Bongo wanda shi kuma ya shafe shekaru 42 yana mulki.

NGUEMA
NGUEMA

Jama’ar kasar sun yi na'an da juyin mulkin cikin farin cikin suka nuna murnar su a Libreville babban birnin kasar, kuma a ranar 4 ga watan Satumba alkalai suka rantsar da Janar Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban rikon kwarya, inda ya yi alkawarin cewa za'a gudanar da sahihan zabuka cikin 'yanci da adalci, amma bai bayar da ainihin lokacin shirya su ba.

Wakilin musamman na Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a Afirka ta Tsakiya Abdou Abarry, ya samu ganawa da Nguema a Libreville a ranar Laraba inda ya shaida masa cewa Majalisar Dinkin Duniya za ta taimaka wa kasar yayin da ta fara wani sabon babi.

Bongo, yana tsare a cikin gida
Bongo, yana tsare a cikin gida

“Da zarar mun san shirin da kuka yi, yanayin lokaci, da lokacin nada gwamnati, hukumominmu daban-daban za su yi tuntuba don su ci gaba da tallafa wa Gabon,” in ji shi bayan ganawar tasu, a wani jawabi da aka watsa a gidan talabijin na Gabon 24.

Ba kamar Nijar ba, ‘yan kasar Gabon ba su nuna kyama ga Faransa ko nuna daukaka ga Rasha ba, kuma manyan hafsoshin sojin da ke Libreville sun nuna a shirye suke domin tattaunawa da kungiyoyin kasa da kasa, inda takwarorinsu na Yamai su suka yi watsi da hakan.

GABON
GABON

Kungiyar kasashen Afrika ta tsakiya ECCAS ta dakatar da kasar Gabon a ranar Litinin, amma ta tura shugaban kasar Afrika ta tsakiya Faustin-Archange Touadera a matsayin wakilinta domin ganawa da Nguema.

Touadera ya shaida wa manema labarai cewa ya kuma samu ganawa da Ali Bongo, da izinin Nguema. Bai bayyana wani cikakken bayani game da halin da Bongo ke ciki ba ko kuma halin da ake ciki ba, yana mai cewa taron ya yi tasiri.

Bongo ya kasance cikin daurin talala bayan juyin mulkin, sai dai a wata sanarwa da Gwamnatin mulkin soji ta fitar a ranar Larabar da ta gabata ta ce yanzu yana da 'yanci kuma yana iya tafiya kasar waje domin duba lafiyarsa idan ya so.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG