Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Addu'o'i Da Mabiya Addinin Kirista Suka Yi Kan Juyin Mulkin Nijar

Mabiya Addinin Kirista Daga Wasu kasashe Sun Yi Taron Gudanar Da Addu’o’i Akan Yanayin Nijar
Mabiya Addinin Kirista Daga Wasu kasashe Sun Yi Taron Gudanar Da Addu’o’i Akan Yanayin Nijar

Kiristoci daga Najeriya, Nijar da Chadi sun shafe kwanaki bakwai suna gudanar da addu'o'i ga kasar ta Nijar dama Nahiyar Afrika baki daya.

AGADEZ, NIGER - Al'ummar Kiristoci daga kasashen Najeriya, Nijar da Chadi sun gudanar da wani taron addu'o'i saboda halin da kasar Nijar ke ciki tun bayan juyin mulki da aka yi, da nufin neman maslaha ga rikicin.

Kiristoci daga kasashen sun shafe kwanaki bakwai suna gudanar da addu'o'i ga kasar ta Nijar dama Nahiyar Afrika baki daya.

Mabiya Addinin Kirista Daga Wasu kasashe Sun Yi Taron Gudanar Da Addu’o’i Akan Yanayin Nijar
Mabiya Addinin Kirista Daga Wasu kasashe Sun Yi Taron Gudanar Da Addu’o’i Akan Yanayin Nijar

Hambarar da Gwamntin Mohamed Bazoum da sojojin Nijar suka yi ya jefa yankin Afirka ta yamma cikin rikici bisa lura da wadannan matsalolin da ka iya samun Afirka ta yamma da kuma ganin an kasa samun maslaha a tsakanin masu shiga tsakani bayan juyin mulkin.

Mabiya Addinin Kirista Daga Wasu kasashe Sun Yi Taron Gudanar Da Addu’o’i Akan Yanayin Nijar
Mabiya Addinin Kirista Daga Wasu kasashe Sun Yi Taron Gudanar Da Addu’o’i Akan Yanayin Nijar

Kusan Kiristoci fiye da 300 ne da suka fito daga kasashen uku don halartar taron addu’o’in, inda wata ‘yar tarayyar Najeriya da ta halarci taron ta ce “na zo ne daga Najeriya domin na halarci wannan taron addu’o’in don yanayin da kasar Nijar ke ciki, yanzu ya zama wajibi a dukufa ga addu’o’i kuma abu ne da ke bukatar gudunmawar kowa dan samun masla a tsakanin bangarorin dake takaddama.”

Kunbai Kiristian wanda shine shugaban wata cocin Evangalika a kasar Chadi ya bayyana fatan a warware rikicin kasar cikin lumana ba tare da an zubda jini ba don gudun jefa yankin Sahel cikin wani rikici na daban.

Mabiya Addinin Kirista Daga Wasu kasashe Sun Yi Taron Gudanar Da Addu’o’i Akan Yanayin Nijar
Mabiya Addinin Kirista Daga Wasu kasashe Sun Yi Taron Gudanar Da Addu’o’i Akan Yanayin Nijar

Ya ce, "babu shakka muna bukatar agajin ubangiji domin ganin Nijar ta ci gaba da tafiya kan tafarkin da aka santa a can baya wato tafarkin zaman lafiya da samun ci gaba kasar wanda yake muhimmancin gaske a tsakanin mabiya addinin Kirista, dan haka ba za mu so mu ga kasar Nijar a cikin wannan yanayin ba saboda haka ne ma muka zo nan domin yin addu’ar fatan an warware matsalar cikin ruwan sanyi."

Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:

Taron Addu'o'i Da Mabiya Addinin Kirista Suka Yi Kan Juyin Mulkin Nijar.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG