Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum Zai Iya Shiga Shafukansa Na Google Ba Tare Da Password Ba


google
google

Kamfanin Google ya tabbatar da cewa ya fara gwadon wasu hanyoyi da mutum zai iya shiga shafukansa na google ba tare da ya rubuta kalmar sirru ba wato password. Mutanen da kamfanin ya gayyata domin su gwada wannan sabuwar hanyar, an aiko musu da sako ne ta wayar hannu inda zasu iya amincewa da sakon kafin su sami izinin shiga account din su.

Wannan sabuwar hanya dai tayi kama da wata hanya da Yahoo ya fitar a kwana kwannan nan, wanda yake shima sako ne za’a aiko wa mutum ta wayar hannu wato puch notification, sannan ka bude sakon ka amince ko kaki amincewa.

Yin amfani da wannan sabuwar hanya wajen shiga rubun bayanan mutum cikin Google ba tare da an rubuta password ba kamar yadda aka saba a baya, ana ganin zai taikamawa mutane wajen rage bata lokaci.

Mutum zai rubuta adireshin email dinsa ne kawai alokacin da yake son shiga cikin bayanansa na Google, bayan haka kuma sako zai shigo wayar mutum yana nunin cewa kaine kake so ka shiga? Idan ka amsa da cewa kaine nan da nan sai ka shiga.

Wannan sabuwar hanyar dai zata taimakawa mutanen da suke da na’urori da yawa, da ma wasu masu rubuta Kalmar sirri mai tsawo da hade haden haruffa, wanda wani lokaci ke da wahalar rubutawa.

XS
SM
MD
LG