Tarihin jami’an tsaro na 'yan sandar jihar New York City, da ake kira Depatment of Police (NYPD). ba zai taba cika ba, batare da ambaton sunan Mrs. Olufunmilola Obe, domin kuwa ta kasance tana aiki da hukumar na tsawon shekaru masu dama.
A karon farko an karramata inda aka karamata matsayi, daga matsayin mataiamakiyar Insfecto, zuwa cikakkiyar Insfecto. An bayyatar da wannan karin girman ne a dai-dai lokacin da ake bukin karrama wasu jami’an ‘yan sanda da sukayi rawar gani a wajen kawo zaman lafiya a ciki da wajen jihar.
Anyi wannan bukin ne a babbar shelkwatar ‘yan sanda a birnin Manhattan. A kuma lokacin wannan bukin an bayyanar da Mrs. Obe, a matsayin macce mai kamar maza, wajen gudanar da aikin ta a duk lokacin da ta fita, haka kuma ta samu lambar yabo da dama wajen aiwatar da aikin ta batare da ban banci ba.