Tiger Woods yace wannan shekara ta 2015 mai karewa ba ta yi masa dadi ba, amma kuma har yanzu zai iya lashe kowace irin babbar gasar kwallon golf a nan gaba.
Tiger Woods, Ba Amurke, ya samu babbar nasararsa ta karshe ta wasan Golf a gasar US Open ta shekarar 2008, yayin da ya lashe gasar kungiyar kwararrun wasan Golf ta duniya ta karshe watanni 28 da suka shige.
Woods, wanda a da shine dan wasan Golf na daya a duniya, amma a yanzu ya subuto har zuwa matsayin dan wasa na 414, yace yana fatan samun shiga gasar wasan Golf na cin kofin Ryder da za a yi a Minnesota.
A lokacin da yake rubuta bayanin abubuwan da suka faru gare shi a shekarar nan ta 2015 a shafinsa na yanar gizo, Tiger Woods yace, “wannan shekara mawuyaciya ce gare ni, a saboda illolin da na samu a jiki na. N afuskanci sauyin yadda nake bugun kwallo da sanda, na daidaita shi, domin a farkon shekara babu wani kaifin bugun kwallo idan na auna zuwa wani wurin da nake so. Abin takaici shine yadda a duk tsawon shekarar na kasa daidaita bugu na. Jiki na ya kasa daukar nauyin wannan sauyin.
Sau biyu ana yi mini tiyata a gadon baya na.”
Yaci gaba da cewa abinda na fi dokin gani a shekara mai zuwa ta 2016, shine in sake fitowa kamar da. Ina kewar buga kwallon golf, kuma ina son in yi ba tare da wani ciwo a jiki na ba.
Game da makomarsa nan gaba a wannan wasa na Golf, Woods ya ce yana son ya tsinci kansa nan da shekaru biyar zuwa 10, yana wasan Golf sosai, yana lashe manyan wasannin Golf na duniya.