Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Ja Hankali Kan Karuwar Mace-Macen Kananan Yara A Sudan


Sudan
Sudan

Sama da kananan yara 1,200 ne suka mutu sakamakon cutar kyanda da tamowa a sansanonin ‘yan gudun hijirar Sudan, yayin da wasu dubbai da suka hada da jarirai ke fuskantar barazanar mutuwa kafin karshen shekara, in ji hukumomin Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata.

WASHINGTON, D. C. - Kusan watanni shida da aka kwashe ana fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun rundunar RSF, bangaren lafiya na kasar ya fuskanci koma baya saboda hare-haren da bangarorin da ke fada ke kaiwa da kuma karancin ma'aikata da magunguna, inji su.

Khartoum, Sudan
Khartoum, Sudan

Dr. Allen Maina, babban jami'in kula da lafiyar jama'a a hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR), ya shaida a taron Majalisar Dinkin Duniya a Geneva cewa yara fiye da 1,200 'yan kasa da shekaru biyar ne suka mutu a jihar White Nile tun daga watan Mayu. Ya kara da cewa "Abin takaici shi ne akwai fargabar adadin zai ci gaba da karuwa."

‘Yan kasar Sudan suna gudun hijira zuw Chad
‘Yan kasar Sudan suna gudun hijira zuw Chad

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta ce ta damu matuka dangane da hasashen cewa "dubban jarirai" daga cikin jarirai 333,000 da za a haifa kafin karshen shekara za su mutu.

Darfur, Sudan,
Darfur, Sudan,

"Jariran da iyayensu mata na bukatar kulawa ta musamman a lokacin haihuwa. Ko da yake a kasar da miliyoyin mutane ko dai suka makale a yankunan da ake yaki ko kuma suka rasa muhallansu, kuma inda ake fama da karancin magunguna, samun irin wannan kulawar zai yi wuya," in ji kakakin UNICEF James Elder a lokacin taron.

Wasu yara - AFP
Wasu yara - AFP

A kowane wata, kimanin yara 55,000 ne ke bukatar magani don cutar tamowa mafi muni da aka gani a Sudan, amma bai wuce daya cikin cibiyoyin samar da abinci mai gina jiki 50 da ke aiki a Khartoum babban birnin kasar, daya cikin goma kuma a jihar West Darfur, in ji shi.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG