Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun Adawan Sudan ta Kudu Ya Amince Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya


Wasu 'yan sakar Sudan ta Kudu sun yi zanga zangar neman zaman lafiya
Wasu 'yan sakar Sudan ta Kudu sun yi zanga zangar neman zaman lafiya

Wani jami’in gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ya bayyana cewa shugaban ‘yan tawayen kasar Rick Marchar ya amince zai sa hannu akan yarjejeniyar samar da zaman lafiya da za ta kawo karshen yakin shekaru 5 da aka kwashe ana gwabzawa a kasar.

Ya dai amince ne kwana daya bayan da ya ki yin hakan.

Tawagar ta Marcher karkashin jamiyyar sa da ake kira SPLM da masu shiga tsakani daga bangaren Shugaba Salva Kirr sun kwashe makoni a birnin Khartoun suna yin shawarwari domin cimma matsaya ta karshe akan yarjejeniyar samar da zaman lafiya da za ta kawo karshen yakin da suke gwabzawa tsakanin su. Yakin ya yi daliln kashe dubban mutane a cikin kasar kana ya bar sama da miliyan 4 da basu da matsugunni.

Wannan dai ba shine karo na farko ba da sassan biyu suka sa hannu na kawo karshen wannan yaki ciki ko harda dakatar da bude wa juna wuta, tare da raba madafan iko a cikin watan Yuni, wannan ne yasa har Machar ya dawo Juba a matsayin mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu na farko.

Da farko dai a ranar Talata Marchar ya ki ya sa wa wannan yarjejeniyar hannu bayan gwamnati ta sa hannu.

Amma Ministan harkokin wajen kasar Sudan Al-Diriri Mohammed Ahmed ya fada jiya Laraba cewa Marchar zai sa wa yarjejeniyar hannu yau Alhamis a Khartoun

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG