Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir ya ayyana dokar ta-baci a jihar da ya fito ta Gogrial da wasu jihohi uku, inda rikici yaki-ci-ya-ki-cinyewa har na tsawon wasu watanni tsakanin mayakan sa-kai na wasu kabilu.
Ministan yada labaran kasar, Michael Makuei, ya ce za a bai wa dakarun kasar karfin ikon tsayar da fadan a jihohin Gogrial da Tonj da Wau da kuma Aweil da suke gabashin Sudan ta Kudu.
Ministan ya fadawa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa, za a jingine wasu ‘yancin walwalar jama’a yayin kokarin tsayar da wannan fada, sai dai bai yi karin bayani kan wannan ikirarin ba.
Akwai rahotanni dake nuna cewa ana yin artabu a jihar Gogrial tsakanin mayakan sa-kan ‘yan Apuk da kuma Aguok wadanda dukkaninsu ‘yan kabilar Dinka ne.
Facebook Forum