Wannan bayanin ya fito ne daga bakin wasu mutane biyu da suke da masaniya kan lamarin wadanda suka yi magana da kamfanin dillanci labarai na Associated Press bisa sharadin sakaya sunansu.
Sai dai an ci gaba da sirranta zargin tuhumar kan Trump Organization da babban jami’in mai kula da harkokin kudi, Allen Weisselberg a ranar Laraba.
Trump ya ce kamfaninsa bai aikata wani laifi ba kuma ya yi shakulatin bangaro ga binciken a matsayin bita-da-kullin siyasa.
Binciken ya hada da abin da kamfanin ya bawa shugabanninsa, ciki har da amfani da gidaje da motoci da biyan kudin makaranta.