Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Kai Karar CNN Kotu Bisa Zargin Bata Masa Suna


Tsohon Shugaban kasar Amurka Donald Trump
Tsohon Shugaban kasar Amurka Donald Trump

Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kai karar gidan talabijin na CNN bisa zargin bata masa suna, ya kuma nemi a biya shi diyyar fiye da dala 75,000 da kuma diyya ta dala miliyan 475, a cewar wata karar da aka shigar a yau litinin, kamar yadda CNN ta rawaito.

Trump yana da'awar cewa, babban gidan labaran ya cutar da sunansa ta hanyar "karya, batanci, da kuma bata masa suna" kuma wannan halin CNN ne "don suna neman yin katsalandan ga harkokin siyasarsa."

Musamman ma, Trump ya ce yana da hakkin a biya shi diyyar daruruwan miliyoyin daloli saboda yadda CNN ta yi amfani da kalmar "Babbar karya" don kwatanta taken Trump game da amincin tsarin zaben shugaban kasa na 2020. Lauyoyin Trump sun ce "Babbar karya" "na nufin dabarar da Adolf Hitler ya yi amfani da ita da kuma fitowa a cikin kanfen mai taken "Mein Kampf" na Hitler.

''Idan kuka fadi kalman karya kuma kuka ci gaba da maimaita ta, a karshe mutane za su yarda da ita,'' in ji lauyoyin Trump, inda suka ce Hitler ya yi amfani da ita wajen haifar da kiyayya ga Yahudawa da kuma ba da hujjan kisan gillar da aka yi musu.

Karar ta ce, "Kamfen din na CNN ta hanyar batanci ga [Trump] ya ta'azzara ne a 'yan watannin nan yayin da CNN ke fargabar shi Trump din zai tsaya takarar shugaban kasa a 2024."

Tun a watan Nuwamban 2020 ne tsohon shugaban kasar ke ikirarin cewa an tabka magudi a zaben, duk da kararrakin da aka yi da kuma sake kirga kuri’un da aka gano ba a yi ba. Majalisa da gwamnati na bincikensa kan yunkurin murde sakamakon zaben, kuma bayan shekaru biyu ya cigaba da ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben 2020.

CNN dai ba ta ce uffan ba game da karar.

An kai karar gaban alkalin da Trump ya nada Raaj Singhal, a gundumar Kudancin Florida.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG