Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ni Na Bada Umurnin Bincike Gidan Trump-Atoni Janar Na Amurka


Merrick Garland
Merrick Garland

Atoni-Janar na Amurka Merrick Garland ya fada jiya Alhamis cewa da kansa ya bai wa masu bincike gwamnatin tarayya izinin neman sammacin kotu don bincikar gidan tsohon shugaban kasar Donald Trump a jihar Florida, dangane da binciken da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta FBI ke gudanarwa kan yadda Trump ya tafiyar da bayanan fadar White House.

A cikin wata ‘yar gajeriyar sanarwar da aka watsa ta gidan talabijin, Garland ya sanar da cewa Ma’aikatar Shari’a ta bukaci wata kotun tarayya da ke Florida da ta buga sammacin binciken da kuma takardar kadarori da aka bai wa wakilin Trump.

Garland ya ce “Ma’aikatar ta yanke shawarar shigar da karar ne don bayyana sammancin ga jama’a da kuma takardar shaidar da tsohon shugaban ya yi a bainar jama’a game da binciken, yanayin da ke kewaye da shi, da kuma babbar maslahar jama’a game da wannan al’amari.”

Da yake kare matakin da ma’aikatar shari’a ta yanke na bincikar gidan Trump, Garland ya ce “ma’aikatar ba ta daukar irin wannan mataki da wasa.”

Kalaman atoni-janar din sun zo ne bayan da ‘yan siyasar jam’iyyar Republican suka yi tir da binciken da aka yi a gidan Trump a ranar Litinin da ta gabata a matsayin amfani da ma’aikatar shari’a don cimma manufar siyasa.

XS
SM
MD
LG