Wannan hanyar de itace fitatciya da ta hada Abuja da jihar Nasarawa da duk jihohin dake arewa maso gabas,inde ba’a kawo batun tanan ne kade hanya shararra zuwa Filato da Benue ba.
Ministan Abuja, Bala Muhammad,yace za’a kaurar da tashar motar Nyanya don rage cunkoson jama’a dake kawo matukar tafiyar hawainiyar motoci.
Wannan hanyar de dake waje da Abuja ta ratsa ta Maraba inda dunbin ma’aikatan Abuja ke zama saboda gujewa tsadar hayar gidaje a cikin gari,wannan anguwar de na cikin jihar Nasarawa ne inda gwamna Tanko Almakura yayi alwashi kamala wata babbar kasuwa don kawarda ‘yan kasuwar dake cunkushe gefen hanyar.
Gwamnar ya kara da cewa”daya da cikin abubuwan da yasa muka karfafa kamala kasuwan shine tausayawa da muke yiwa ‘yan kasuwa kanana wadanda suke baza kolin su a gaban hanya ba inda zasu je,kuma yau a tashe su gobe a barsu jibi a tashe su wannan ma kadai yana karya jali,shi yasa muke so muyi wannan na masamman."
Wannan hanyar de saboda yawan jama’a, a cunkushe take kusan kowane lokaci, ga Babura barkatai dage jigilar jama’a.