Yau Lahadi kasar Kuwait tace ta gano cewa wani Balaraben kasar Saudi Arabiya mai suna Fahd Suleiman Abdulmoshen Al Qaba'a, shine dan harin kunar bakin waken daya kai harin wani Masalacin yan Shiya dake cike da mutane, ya kashe akalla mutane ashirin da shidda da raunana wasu da dama.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Kuwait tace Fahd Suleiman Abdul Moshen Al Qaba'a shine keda alhakin kai hari Masalacin na 'yan Shya a cikin wanna wata na Ramadan.
Jiya Asabar Prime Ministan Tunisia Habib Essid yayi kokarin inganta matakan tsaro a yayinda dubban yan yawon bude ido yan kasashen waje suka fice daga kasar bayan da aka kai hari wani wurin shakatawa na gabar teku. Mr. Essid ya bada umarnin a tura sojojin wucin gadi zuwa otel otel da wasu wuraren yawon bude ido, ya kuma ce za'a rufe kimamin Masalatai tamanin a kasar.
Akalla mutane talatin da takwas aka kashe wasu da dama kuma suka ji rauni a ranar Juma'a, lokacinda wani matashi dan kasar da yayi shigar burtu kamar mai yawon bude ido ya bude wuta a otel din marhaba na gabar teku.