Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kerry Ya Gana Da Hadi a Saudiyya


Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry a lokacin ziyarar da ya kai Saudiyya
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry a lokacin ziyarar da ya kai Saudiyya

Sakataren harkokin wajen Amurka na yunkuri ya kawo karshen kai hare-hare a Saudiyya bayan rikicin siyasar kasar da ya barke na wasu tsawon watanni.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya yi wata tattaunawa da ya kira mai muhimmanci yau Alhamis tare da shugaban kasar Yamal Abdu Rabbu Mansour Hadi, yayin da ya ziyarci Saudi Arabiya don tattaunawa akan shawarar dakatar da kai hare-hare a Yamal inda dakarun kasashen da Saudi ke jagoranta ke kai farmaki da jiragen yaki na saman.

Mr. Hadi ya tsere zuwa kasar Saudiyya a karshen watan Maris lokacin da ‘yan tawayen Houthi daga Sana’a babban birnin kasar suka kutsa zuwa kudancin kasar, matakin da ya sa jiragen saman yakin Saudi Arabiya kaiwa ‘yan tawayen hari da bam.

Amma kungiyoyin ba da agaji sun yi korafi akan irin matsalolin da ake samu wajen yin jigilar kayayyakin abinci da na masarufi ga ‘yan kasa.

Mr. Kerry ya fada jiya Laraba cewa in za a dakatar da hare-haren ta sama to dole ne a yi hakan ba tare da ba wani damar kwace yanki ba ko kai hari akan wadanda suka ajiye makaman su.

Mr. Kerry ya kuma ce, sun yi kira ga duk bangarori, da duk wadanda abun ya shafa da su bi dokokin ba da taimako su kuma dauki duk matakin da ya kamata don kawar da farar hula a inda ake kai harin, ko inda za a taba su, su kuma su ba da damar ganin an rarraba kayyakin agaji.

A jiya Alhamis, sakataren ya gana da sabon ministan harkokin wajen Saudi Abdel al-Jubeir kuma an shirya zai gana da sarki Salman.

XS
SM
MD
LG