Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan yakin sa kai a kasar Yamal sun kwace wani muhimmin sansanin soja a kudancin kasar


Mayakann kungiyar Al Qaida
Mayakann kungiyar Al Qaida

Jiya Juma'a, yan yakin sa kan kungiyar Al Qaida a kasar Yamal suka kwace wani muhimmin sansanin soja a birnin Mukalla dake kudancin kasar, bayan da suka karfafa rike birnin da kuma mamaye tashar jiragen ruwa dake birnin.

Jiya Juma'a, yan yakin sa kan kungiyar Al Qaida a kasar Yamal suka kwace wani muhimmin sansanin soja a birnin Mukalla dake kudancin kasar, bayan da suka karfafa rike birnin da kuma mamaye tashar jiragen ruwa dake birnin.
'Yan yakin kan sun dauki wannan mataki ne kwana daya bayan da suka kutsa gidan yarin dake yankin suka kubutar da fursunoni dari uku. Jami'an sojan Yamal sunce turjewa ko kuma bijirewa kalilan yan yakin sa kan suka fuskanta a lokacinda suka kutsa gidan yarin.
Daga yammaci kasar kuma sojojin kawance na taron dangi karkashin jagorancin kasar Saudi Arabiya suna kokarin tare danawar da yan Houthi keyi, sun kuma jefowa mayakan dake fafatawa da yan tawayen Houthis makamai a birnin Aden mai tashar jiragen ruwa dake kudancin kasar.
Mai magana da yawun sojojin kawance Janaral Ahmed Assiri yace makaman da aka jefowa mayaka ya taimaka wajen canja yadda al'amurra suke a kasa. Mazauna birnin Aden sunce jiya Juma'a yan Houthis suka janye daga daya daga cikin fadan shugaba Abdu Rabbo Masur Hadi da suka mamaye.
Haka kuma fafatawa a titunan ya zafafa jiya Juma'a a birnin Aden, inda sojojin dake biyaya ga shugaba Hadi suka yi kokarin hana 'yan Houthis kwace birnin, baban birnin na karshe dake hannun magoya bayan shugaba Hadi. Bugu da kari, jiragen saman yakin sojojin kawance sun kai hare hare.

XS
SM
MD
LG