Hare haren da dakarun hadin guiwa karkashin jagorancin Saudi Arabiya suke kaiwa ta sama kan ‘yan tawayen Houthi a Yemen ya gaza hanasu kutsawa cikin kasar.
‘Yan tawayen Shi’a da dakaru abokan kawancensu, sun fadada wuraren da suke kai farmaki jiya Alhamis a tsakiyar sasssan birnin Aden,da kuma yankunan kudu maso gabashin kasar da galibi ‘yan sunni ne.
Jiya Alhamis, kakakin dakarun hadin guiwa na Saudiya, Ahmed al-Asiri ya musanta cewa ‘yan tawayen suna kara kutsawa, yace, mayaka kalilan da suka ware, sun kara gaba, kuma za a kawar da su. Yace an katse hanyoyin sadarwa tsakanin ‘yan tawayen.
Bisa ga rahoton kamfanin dillancin labaran faransa, jiya Alhamis dakarun karkashin jagorancin Saudiya suka kai hari kan ginin ma’aikatar tsaron kasar dake Sana’a babban birnin kasar, daga cikin jerin hare haren da suka kai kan wuraren da ‘yan tawayen suka ja daga a kewayen birnin.
Shugaban addinin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya danganta hare haren da Saudi Arabiya take kaiwa da kisan kiyashi, ya kuma gargadi Riyadh da ta daina “aikata miyagun laifuka”.
Tehran, da ake kyautata zaton tana goyon bayan ‘yan Houthi,tace zata tura jiragen ruwanta na yaki zuwa tekun Yemen. Washington a nata bangaren, ta kara goyon bayan makamai da ayyukan leken asiri da take ba dakarun hadin guiwa karkashin jagorancin Saudiya.
Sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka John Kerry yace Washington ta damu matuka da matakin da Iran ta dauka.