Sanidiyar harin bamabaman yasa gwamnatin jihar ta rufe kasuwar har sai ta kammala kwashe baraguzan shaguna da gidajen da suka ruguje.
Amma yanzu 'yan kasuwar sun bukaci gwamnati da ta bude kasuwar domin rage matsalar rayuwa da suka shiga ciki. Shugaban 'yan kasuwar Abdulrahaman Jimoh Yusuf yace suna rokon gwamnati da ta gaggauta sake bude kasuwar domin rage matsalar rayuwa dasu da iyalansu ke ciki. Yace gwamnati ta taimaka kada mutuwar ta zama kashi biyu. A taimakawa talakawa tare da bude kasuwar domin su cigaba da kasuwanci. Idan suka cigaba da kasuwanci wannan zai nuna kwanciyar hankali.
A cewar shugaban wasu sai sun fito kasuwa zasu samu abun ciyar da iyalansu. Idan ba'a bude kasuwar ba wasu bata gari ka iya sa komi ya faru.
Shi ma shugaban 'yan kasuwa na jihar Filato Mr. Danjuma Hirse ya kira a kara matakan tsaro a kasuwar. Yace sun yi asarar rayuka fiye da dari biyu da dukiyoyi da suka kai nera biliyan daya sabili da haka suna kiran gwamnati ta inganta tsaro a kasuwar. Ya kira hadin kai da jami'an tsaro domin hana sake aukuwar irin abun da ya faru.
Sakataren kungiya agaji ta Red Cross ya ba gwamnatin jihar shawarar gina kasuwanni a anguwanni domin rage cunkoso a kasuwar taminus.
Kawo yanzu dai gwamnati na cigaba da share kasuwar kuma bata bada sanarwar ranar da zata sake bude kasuwar ba.
Ga rahoton Zainab Babaji.