Wata kungiya me zaman kanta a Najeriya mai suna a turance Network for Justice, tayi kira da cewar ‘yan siyasa yakamata su iya bakunan su dan gane da karatowar zabe a kasar. Ganin cewar tun da a kagama zaben 2011 da ya gabata kasar bata sake zama lafiaya ba musamman ma a yankin Arewa. Mal. Aminu Sule wani wakilin wannan kungiyar yace abun da suke haddasa wadanna rigingimu da suka faru a bayan zaben da yagabata shine, ‘yansiyasa sun yi abun da ransu ke so wanda shi ya haifar da wannan rashin kwanciyar hankali a yanki Arewa baki daya. Yace dole ne mu lura don gashi yanzu wani zaben ya tunkaro. Yace ‘yansiyasa yakamata suyi a hankali don kada su sa talakawa cikin wani hali, domin mafi akasarinsu sukan ce sai sun ci zabe koda za’a mutu ne, wanda shike haddasa wadannan rikitutukan. Ya kumayi kira ga hukumomi da suyi zaben gaskia kuma duk wanda yaci kada a murde zabe a bama duk wanda yaci. Yace mahimin abu shine kada a yi amfani da jami’an tsaro wajen murde zabe.
Shi kuma Dr. Sadik Umar Gombe, darecta ne a majalisar samar da daidaito a tsakanin jam’iyu a Najeriya, yace baban dalilin da zai sa a kaucema rikici a wannan zaben mai zuwa, shine a tabbatar da anyi adalci, domin idan al’umah suka zaba abunda suke so kuma aka chanza musu to wannan shi zai haddasa rikici a kasar.