Kungiyar ta bukaci uwar jam'iyyar PDP ta kasa da ta gaggauta fitar da wani dan takara kafin ranar ashirin da shida wannan watan.
A cewar shugaban kungiyar matasan Dalyop Choji Davou jama'a da dama sun koka da rashin adalci a wurin zaben fidda dan takarar a jam'iyyar. Yace dole su nunawa jama'a rashin gamsuwarsu da rashin yaddarsu da matakai da hanyoyi da aka bi domin fitar da dan takarar PDP. Suna karfafawa ne akan PDP domin ba zasu yadda wata jam'iyya ta kafa masu wani gwamnati ba saidai ita PDP din.
Yace a gaskiya ba'a yi zaben fidda gwani ba. Ba'a bi gaskiya ba. Da aka zo zaben fidda gwani sai wakilan sauran 'yan takaran suka gano wani shiri da aka yi domin a yi dauki dora. Sun jawo hankalin wanda aka turo daga Abuja ya gudanar da zaben cewa matakan da aka dauka ba zasu taimaki zaben ba. Amma mutumin yaki ya sauraresu.Dama can gwamnati tana bayan dan takarar da yaci domin sun bi wakilan suna raba masu kudi da tilasta masu suyi rantsuwa zasu zabeshi.
Yakamata uwar jam'iyya ta zauna da duk 'yan takarar da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar su zabo mutum daya da zai tsaya zabe amma ba Sanata Pwajok ba. Mutane sun nuna basa sonshi. Idan PDP ta tsaya a kansa ba zata ci zaben ba. Ya zama masu wajibi su yi wani abu nan da ranar 26 na wannan watan
Shi ma shugaban majalisar matasan Kirista a Najeriya Luka Shehu yace yadda shugabannin ke yin siyasa ka iya raunata dimokradiyar Najeriya. Yace ana neman matsayi ta ko yaya. Babu tsoron Allah. Ana abubuwa kamar tsafi.
Wani dan majalisa kira yayi a nemi sulhu da wadanda aka saba masu a siyasance.
Ga Zainab Babaji da karin bayani.