Kawo yanzu an yiwa kungiyoyi tamanin da biyu rajista a karkashin lemar masu goyon bayan Janaral Buhari.
Wadannan su ne suke jagorancin kimanin kungiyoyi dubu hudu da saba'in da biyar da suka kunshi mambobi miliyan hudu da dubu dari hudu da casa'in da uku da dari biyu da ashirin da shida.
Janaral din ya yi bayanin ne wa manema labarai biyo bayan wani zargi da jam'iyyar PDP tayi inda tace wasu gwamnoni ne musamman Rotimi Amechi na jIhar Rivers ke turawa Buhari kudi da suka diba daga baitul malinsu. Zuwa yanzu mambobin ta hanyar bada nera dari dari sun tara nera sama da miliyan hamsin da hudu.
Janaral Buhari yace magoya bayansa ne zasu cigaba da bada taimako domin kemfen din tunda shi bashi da kamfanoni da ma'aikata sabili da haka ba zata yiwu ba yace mutane su kawo kudi. Amma wadanda suke goyon bayansa zasu sayi katin taimako daga nera dari zuwa dubu goma. Za'a tara kudin a asusun banki kuma shi kadai ne zai iya fidda kudi daga ciki.
Ibrahim Abdulkarim shi ne jami'in kula da tara kudin na Janaral Buhari yace idan mutane miliyan daya suka bada nera dari dari sun tara miliyan dari ke nan. Idan suka ce kullum zasu dinga bada nera dari dari, to cikin kwana talatin za'a tara biliyoyin nera.
A zaben shekarar 2011 Janaral Buhari ya samu mutane miliyan goma sha biyu. Wadannan mutanen sun rubanya yanzu sun kai miliyan talatin. Cikinsu akwai wanda zasu bada dubu daya ko dubu dari ko ma miliyan daya. Daga jiyan yace idan sun dage zuwa biyu ga wata mai zuwa zasu tara nera biliyan ashirin da daya ko fiye ma.
Amma banbancin nasu biliyan ashirin da daya da na PDP shi ne jama'a ne magoya bayan Janaral suka tara maimakon na PDP da suka hada da ma'aikatun gwamnati a wani yanayi da yayi kama da murdiya. Ta APC ta gaskiya ce. Ba kuma zai yiwu ba a hada gaskiya da karya.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.