Yin hakan shi ne na baiwa kowa 'yancinsa domin kaucewa fitinar da kan kawo doguwar nadama.
Duk da wai dattawan suna da katunan shaida jam'iyyunsu amma suna ganin mahimmancin dattaku a yayin kenfen.
Isa Tafida Mafindi na daga cikin dattawan. Yace jam'iyya dake da inuwa babba babu irin mutanen da basa ciki ko PDP ko APC. Kuma wasu idan ba an yi rigima ba basa ganewa. Irin wadannan mutanen ne suke ya kamata a mayarda hankali a kansu. A kundun tsarin mulkin kowace jam'iyya babu inda aka ce a bugi mutum ko a kasheshi. A dokokin zabe da dokokin kasa duk babu wannan ciki. Amma duk wanda yake da muguwar zuciya to ba za'a iya dauke masa ita ba saidai Allah ya kiyaye ya dauke masa. Amma wannan siyasa da ikon Allah za'a yita lami lafiya a kuma fitar da wanda mutanen Nageriya suka zaba.
Wazirin Pindiga Ismaila Muazu Hassan wanda ya samu tikitin neman takarar majalisar wakilai a inuwar PDP na ganin lumana da hangen nesa ne zasu taimaki 'yan siyasa musamman na yankunan dake da'irar fitinar Boko Haram. Ya kira duk al'umma a zo a yi zabe domin abu ne na ra'ayi. Kowa ya bi ra'ayinsa da abun da yake so cikin kwanciyar hankali ba tare da an samu tashin hankali ba. A fara lafiya a gamashi lafiya. Amma wani yace shi kadai ne kuma zai hana wani ba dede ba ne kuma ba za'a yadda dashi ba.
Saidai kuma Dattijo Ustaz Yunus dake takarar majalisar wakilai a inuwar jam'iyyar APC na ganin idan shugabannin koli suka gyaru to kasa ma zata iya daidaita. PDP ta dade tana mulki kuma ba'a ganin cigaba kuma ace alatilas ba zaka fadi albarkacin bakinka ba. Ba zaka yi anfani da 'yancinka ba ka fito ka fadi ra'ayinka?
Ga Nasiru Adamu El-hikaya da karin bayani.