Masanin harkokin nazarin rayuwar dan‘adam da binciken hanyoyin kawo hadin kai da fahimta tsakanin al’umma dake wata jamia’a a Amurka, farfesa Samuel Zalanga, yace akwai bukatar jama’ar Najeriya su kawas da banbance-banbancen dake tsakanin su domin ciyar da kasa gaba, yayi wannan kalamin ne a wata a hira da yayi da muryar Amurka.
Farfesa Zalanga yace, magance matsalolin zabe a kasar shine iya gano hanyoyin da ya kamata a bi ta wajen duban makamantan wadannan matsalolin da suka faru a duniya, ya kuma yi kira ga talakawan Najeriya da su kawas da duk wani bambanci musamman na addini, kabilanci da bangaranci su hada kawunansu don hakan ne kawai zai kawo canji.