Dangane da haka ne hukumar zaben Najeriya ko INEC a takaice, ta daura damarar sanya ido akan yadda 'yan takara da jam'iyyunsu ke kashe kudade wajen yakin neman zabe a kasar.
Hukumar ta lura 'yan siyasa musamman 'yan takara basa mutunta dokoki da ka'idodi da ta shimfida ta fuskar kudade.
Amma Abdullahi Mai Kano Zara wani dan jam'iyyar APC a Kano yace ita hukumar zabe ta yanzu idan ba'a rabata da fadar shugaban kasa ba to wadannan matsaloli ba za'a rabu da ganinsu ba. Yace tsarin da suka shimfida babu wani dan Najeriya da zai iya karbarsa domin daga wurinsu komi ya lalace. Idan Allah ya ba jam'iyyarsu ta APC gwamnatin tarayya to zasu kafa hukumar zabe mai kyau wadda za'a rabata da fadar shugaban kasa domin ta zauna tayi abun da ya kamata. Muddin hukumar tana karkashin fadar shugaban kasa babu abun da zata gayawa 'yan Najeriya su yadda dashi.
Abdulmunmuni Yau Musa na jam'iyyar PDP yace idan aka yi hakan abu mai kyau ne amma da wuya ko a cikin PDP ko APC a ce hukumar zata iya sa ido akan duk harkokin jam'iyyun. Misali a ce za'a sayi motoci na nera miliyan goma ta yaya INEC zata tabbatar motocin jam'iyya ta saya.
'Yan takara ma sun fadi albarkacin bakinsu. Bara'u Jibrin dan takarar APC na zuwa majalisar dattawa daga mazabar Kano ta Arewa yace tunane ne mai kyau amma kuma da wuya ya tabbata. Misali yace kwana kwanan nan PDP ta kaddamar da bikin tara kudi. Jerry Gana ya fito yace shi da abokansa sun bayar da nera biliyan biyar. Tambaya nan ita ce su wanene abokan nasa? Idan hukumar zabe da gaske ta keyi kamata yayi ta fara bincike akan irin wannan lamarin domin a tabbatar da gaskiya kana mutane su yadda da tsarin.
Saidai Malam Albati Bako masanin harkokin dimokradiya kuma mai sharhin kan alamuran zabe yayi tsokaci. Yace tsarin da INEC ta gabatar yana faruwa ne a kasashen da suke da buwaya suka kuma yi shekaru aru-aru suna yin dimokradiya saboda tattalin arzikinsu yana kan takarda. Kowane dan kasa yana da asusu a bankin. Kowace jam'iyya kuma tana da asusu a banki. Saboda haka kowane dan takara an san adadin abun da zai samu a matsayin taimako kuma idan ya tashi ajiyewa ba a gida zai ajiye ba. Amma a Najeriya kashi goma cikin dari ne mutanen dake da asusu a bankuna kamar yadda kiyasin babban bankin Najeriya ya nuna. A cikin irin wannan yanayin zai yi wuya a ce INEC zata iya gano adadin kudaden da 'yan takara ko jam'iyyu zasu kashe har ta san inda suka wuce ka'idar da ta shimfida masu.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.