Zanga-zangar da ta hada da yajin aiki na kwanaki biyar dai ta yi sanadin rufe gidajen mai, asibitoci, bankuna, makarantun gwamnati da sauran cibiyoyin gudanarwa da ke fadin jahar.
Kwamared Ayuba Wabba shine Shugaban kungiyar na kasa kuma shi ya yi jawabi kan dalilin daukan wannan mataki.
Ya ce ba'a taba yajin aikin da hatta jiragen sama da na kasa basa shiga Kaduna ba. Kuma in aka tuna baya an kori mutum dubu biyar wanda har yanzu ba'a biya su ba.
Karin bayani akan: Ayuba Wabba, Kaduna, NLC, Nigeria, da Najeriya.
Shuwagabannin Kungiyar kwadago na kasa da dama sun halarci wannan zanga-zangar a Kaduna kuma sun ce dama alkawari su ka yiwa juna, kuma sun cika alkawarun da suka dauka domin nuna bacin ransu.
Har kungiyar kwadagon ta gama wannan zanga-zangar dai gwamnati ba ce komai ba ko da yake kafin fara wannan zanga-zangar kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jahar Kaduna, Malam Jafaru Sani ya gargadi 'ya'yan ungiyar kwadagon baki daya game da wannan yunkuri.
Duk da fargaban tashin hankali yamutsin da gwamnatin jahar Kaduna ta bayar dai, taron zanga-zangar ya ta shi ba tare da wata bayananniyar matsala ba.
Saurari cikakken rahoton a sauti: