Kungiyar Kwadago ta NLC a Najeriya, ta janye yajin aikin kwana biyar na gargadi da fara a jihar Kaduna.
Janye yajin aikin na zuwa ne yayin da zanga-zanga lumana da ‘ya’yan kungiyar ke yi ta shiga rana uku.
Yajin aikin ya durkusar da harkokin yau da kullum a jihar ta Kaduna, inda bankuna, tashar jirgi, ma’aikatan wutar lantarki da ma na kiwon lafiya suka janye daga wuraren ayyukansu.
Gwamna Malam Nasiru El Rufai, ya zargi kungiyar da kokarin kassara tattalin arzikin jihar, lamarin da ya sa ya ayyana neman shugabannin kungiyar ta NLC ruwa a jallo.
Sai dai bayan wani taron gaggawa da aka yi a daren ranar Laraba, a jihar ta Kaduna da ke arewa maso yammaci Najeriya, shugaban kungiyar NLC Ayuba Wabba, ya ce sun janye yajin aikin.
Rahotanni sun ce NLC ta janye ne don ta amsa gayyatar da gwamnatin tarayyi ta yi na neman a sasanta rikicin.
A ranar Talata gwammatin tarayya ta bayyana shirinta na shiga tsakanin bangarorin biyu bayan da aka kwashe yini uku ana kai ruwa rana.
Ministan kwadago Chris Ngige, ya yi kira ga Gwamna El Rufai da shugaban NLC Wabba da su mayar da wukakensu kube.
Yajin aikin ya samo asali ne bayan da gwamatin jihar ta Kaduna ta salami ma’aikata sama da dubu bakwai.