Shugaban kungiyar kwadago a jihar Nasarawa, Yusuf Sarki Iya ya ce tun farko sun shiga yajin aikin ne saboda gwamnati ta kasa biya masu bukatunsu.
A cewarsa, bukatun sun hada da karin girma ga ma’aikata, rashin bada zarafin kara samun horo wa ma’aikata, rashin biyan karancin albashi na naira dubu talatin da gwamnatin tarayya ta amince da sauransu.
Mai magana da yawun gamayyan kungiyoyin ma’aikatan jinya a jahar Nasarawa, Kyari Caleb ya ce sun lura cewa yarjejeniyar da aka cimma ba ta magance bukatun da suka gabatar ba don haka za su ci gaba da yajin aiki.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce ba zai sa hannu don amincewa da yarjejeniyar ta kungiyar kwadago ba har sai sun sasanta da kungiyar gamayyan kungiyoyin ma’aikatan jinya a jihar.
Yajin aiki da ma’aikata kan shiga a Najeriya, kan zama masu makami wajen neman a biya masu bukatunsu.
Gwamnatoci a lokuta da dam akan zargin ma’aikatan da shiga yajin aikin don cimma burinsu ba tare da suna la’akkari da kuncin da za su jefa al’uma ba.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji: