Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Sabuwa; El-Rufai Na Barazanar Korar Ma’aikatan Lafiya 600


Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

Shugaban kungiyar ma’aikatan jinya da unguwar zoma ta kasa reshen jihar Kaduna, Kwamared Ishaku Yakubu ya ce gwamnatin jihar Kaduna na barazanar sallamar mambobinta 600 daga bakin aikinsu saboda sun shiga yajin aikin kungiyar kwadago ta NLC.

Kwamared Ishaku Yakubu wanda ya tabbatar da hakan ga yan jarida a ranar Laraba, ya ce tuni gwamnatin jihar ta ba da umarnin tattara bayanan mambobin kungiyar ta da ke aikin jinya dubu 1,300.

Ya ce bayan kammala tattara bayanai da sunayen kuma, gwamnatin ta ce za ta rage adadin ma'aikatan zuwa 600 daga bisani.

A ranar 18 ga watan Mayun nan da ya shige ne gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna ya sanar da sallamar dukkan ma’aikatan jinyar wadanda ke kasa da matakin albashi na 14 a Jihar saboda shiga yajin aikin gargadin da kungiyar kwadago ta Kasa wato NLC ta yi a jihar, kafin gwamnatin tarayya ta shiga tsakani bayan kwanaki 3 ta janye yayin aikin.

Rahotanni daga jihar Kaduna sun bayyana cewa, gwamna Nasir El-Rufai ya ba maiakatar lafiya ta jihar umarnin ta tallata guraben aiki domin dibar sabbin ma’aikatan da za su maye gurbin wadanda aka kora.

Shugaban kungiyar ta NANNNM, Kwamared Ishaku Yakubu ya nuna damuwa ga bayanai da ke nuni da cewa, ya zuwa yanzu gwamna El-Rufai na nan a kan bakarsa kan korar ma’aikatan da suka shiga yajin aikin wanda ya ce ya saba ka’ida da kuma gurgunta ayyukan bunkasa tattalin arziki a jihar.

Kwamared Ishaku Yakubu ya ce gwamnatin jihar Kaduna ta cire sunayen ma’aikatan jinya da ke hutunsu na shekara a halin yanzu, wadanda suka tafi karo karatu da wadanda ke hutun haihuwa har ma da wasu mutane biyu da ’yan bindiga suka sace makonni bakwai da suka gabata a cikin jerin sunayen ma’aikata da ke cikin rijistar ma’aikatan jinya da ungunzoma ta jihar.

Ya kara da cewa tuni suka dauki matakin sanar da uwar kungiyar su a matakin kasa a kan yunkurin gwamna Nasir El-Rufai na kwacewa mambobin kungiyarsu hanyar samun na kai bakin salati.

A lokacin hada wannan labari, duk kokain jin ta bakin gwamantin jihar Kaduna kan wannan lamarin ya ci tura.

XS
SM
MD
LG