Kungiyar ta Masiyawa wadda ta kira wani taron manema labarai a Zaria, ta ce ilmantar da mabiyanta da yada bishara su ne manyan ayyukan da ta sa a gaba, a cewar shugaban kungiyar Farfesa Dauda Ishaya.
Farfesa Ishaya ya ce yada bishara a cikin yarukan guda uku, da taimakon kai da kai, da kuma ilmantar da 'yayan kungiyar wajen koya musu karatu da rubutu da ma ayyukan lafiya su suka fi maida hankali akai.
Bangaren mata da matasa na kungiyar ta Masiyawa ma ya ce nasara na kara samuwa ga kungiyar.
Hajara Sama'ila Mamman, ita ce shugabar mata ta kasa a kungiyar, ta ce suna samun ci gaba musamman ta fannin wakilcin mata a kowace jiha, abin da ke basu damar shiga yankunan karkara don ilmantar da mata ayyukan hanu da kuma fadakar da su game da cututtukan da ke damunsu.
Yakubu Ezekiel Madaki, shi ne shugaban matasa na kungiyar, ya ce sukan janyo matasa 'yan uwansu su ilimantar dasu su kuma nuna musu hanyoyi masu kyau.
Sai dai kuma shugaban kungiyar, Farfesa Ishaya ya ce kungiyar na fama da wasu matsaloli, kamar rashin kudi, rashin abun hawa, nuna wariya da kyama daga Kiristoci 'yan kudu.
Mutanen kudancin Najeriya da yawa dai na ganin duk bahaushe ko bafulatani a matsayin Musulmi, abin da ake ganin kuma shi ke kawo kyamar Kiristoci Hausawa daga Arewa idan suka je kudancin Najeriya.
Saurari rahoton cikin sauti: